Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Tashar 13 ta gidan talabijin na Ibraniyawa ta ba da rahoton cewa sojin gwamnatin Sahayoniya da hedkwatar rundunar tsakiya ta sojin Amurka (CENTCOM) sun amince da tsara shirye-shiryen haɗin gwiwa da nufin tunkarar duk wata yiwuwar tsanantar tashin hankali kan Iran.
Wannan tashar ta bayyana cewa sojin gwamnatin Sahayoniya sun ba da labarin kasancewar haɗin gwiwar shirye-shirye da Amurka wajin fuskantar yiwuwar tsanantar tashin hankali kan Iran kuma sun yi iƙirarin cewa ƙarshen wa'adin yaƙin ya kusanto.
Tashar 13 bisa bayanin wani babban hafsan Sahayoniya da ba a bayyana sunansa ba, ta ba da rahoton cewa a cikin ziyarar "Brad Cooper" kwamandan CENTCOM zuwa Tel Aviv ba a yi magana kan yanke shawara don kai hari Iran ba.
Wannan tashar ta kuma ƙara da cewa kiyasin tsaro yana nuni da cewa yiwuwar sake fara yaƙi kan Iran idan aka kwatanta da kwanakin da suka gabata, bai ƙara kusanta ba. Ana kiyasta matakin shirin gwamnatin Sahayoniya a matsayin mai girma, ko da yake bai kai matakinsa mafi girma ba.
Dangane da wannan rahoto, kiyasin sojin gwamnatin Sahayoniya yana nuni da cewa lokaci ya yi da "Donald Trump" shugaban Amurka zai yanke shawara kan mataki kan Iran.
Taron Ɓangarori Uku Na Shugabannin Soji Da Bayanai A Tel Aviv
Ranar Laraba, "Brad Cooper" a Tel Aviv ya gudanar da taro na ɓangarori uku da "Eyal Zamir" shugaban hafsan sojin gwamnatin Sahayoniya da "Roman Goffman" shugaban hukumar leƙen asirin waje ta gwamnatin Sahayoniya (Mossad). An gudanar da wannan taro ne a yanayin da wannan gwamnatin ta ke ƙara shirye-shiryen sojinta ga yiwuwar sake fara hare-hare kan Iran.
Sojin gwamnatin Sahayoniya a cikin wata sanarwa sun bayyana cewa Zamir da Cooper sun kuma gudanar da haɗaɗɗen kiyasin hasashe kan halin da ake ciki kuma sun tattauna kan abubuwan da ke faruwa a yankin da ƙalubalen tsaro na haɗin gwiwa.
A cikin wannan taro, "Itzik Cohen" shugaban sashen ayyuka na sojin gwamnatin Sahayoniya, "Heidi Zilberman" shugabar sashen shirye-shirye, "Shlomi Binder" shugaban sashen bayanan soji, "Omer Tishler" kwamandan sojin saman gwamnatin Sahayoniya da wasu kwamandojin ɓangarorin biyu sun halarta.
A ci gaba da sanarwar sojin gwamnatin Sahayoniya an ce mahalarta sun tattauna kuma sun yi musayar ra'ayi kan muhimmancin zurfafa haɗin gwiwar dabarun da na aiki tsakanin sojojin biyu, ƙarfafa daidaitawa da ƙara matakin shirin haɗin gwiwa wajin fuskantar nau'ikan yanayi daban-daban.
Duk da haka, a cikin wannan sanarwa ba a bayyana abin da ake nufi da yanayin da aka tattauna ba ko kuma ko tattaunawar ta shafi batun Iran kai tsaye ba.
Rahoton Kafar Watsa Labarai Ta Sahayoniya Kan Nazarin Shirin Sake Yaƙi Da Iran
Jaridar Ibraniyawa "Yedioth Ahronoth" ranar Laraba ta ba da rahoton cewa a cikin taron Cooper da Zamir, an nazarci matakin shirin sojojin biyu ga yiwuwar sake fara yaƙi kan Iran idan ya zama dole.
An gudanar da wannan taro ne a yanayin da kafofin watsa labarai na gwamnatin Sahayoniya suka wallafa rahotanni kan shirye-shiryen soji ga yiwuwar sake fara hare-hare kan Iran.
..............................
Ra'ayinka